Ish 44:6-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ubangiji, wanda yake mulkin Isra'ila, ya kuma fanshe su,Ubangiji Mai Runduna, yake faɗar wannan,“Ni ne farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici,Ba wani Allah sai ni.

7. Ko akwai wanda zai iya yin abin da na yi,Ya kuma fito fili ya faɗi abin da zai faruTun daga farko, har zuwa ƙarshe?

8. Ya jama'ata, kada ku ji tsoro!Kun sani tun daga zamanin dā can, har zuwa yanzu,Na faɗa tun da wuri abin da zai faru.Ku ne kuwa shaiduna!Ko akwai wani Allah?Ko akwai wani Allah mai iko da ban taɓa jin labarinsa ba?”

9. Dukan waɗanda suke ƙera gumaka mutanen banza ne, gumakan da suke sa wa kuɗi da tsada kuma aikin banza ne. Waɗanda suke yi wa gumaka sujada kuwa makafi ne su, jahilai, za su sha kunya.

10. Wannan aikin banza ne, mutum ya yi siffa da ƙarfe don ya yi mata sujada!

Ish 44