1. Ya Isra'ila, Ubangiji wanda ya halicce ku ya ce,“Kada ku ji tsoro, na fanshe ku.Na kira ku da sunanku, ku nawa ne.
2. Sa'ad da kuke bi ta cikin ruwa mai zurfi,Zan kasance tare da ku,Wahala ba za ta fi ƙarfinku ba.Sa'ad da kuke bi ta cikin wuta, ba za ku ƙuna ba,Wuyar da ta same ku ba za ta cuce ku ba.
3. Gama ni ne Ubangiji Allahnku,Allah Mai Tsarki na Isra'ila, wanda ya cece ku.Zan ba da Masar, da Habasha, da SebaGa Sairus domin fansarku.
4. Zan ba da dukan al'ummai don in ceci ranku,Gama kuna da daraja a gare ni,Gama na ba ku girma, ina kuma ƙaunarku.