Ish 42:21-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Ubangiji shi Allah ne da ya ƙosa ya yi ceto saboda gaskiyarsa,Saboda haka yana so a girmama koyarwarsa,

22. Amma yanzu an washe mutanensa,Aka kukkulle su a kurkuku,Aka ɓoye su a rami.Aka yi musu fashi, aka washe su,Ba wanda ya zo domin ya kuɓutar da su.

23. Ko akwai wanda zai kasa kunne ga wannan?Ko za ku kasa kunne ku yi lura daga yanzu?

24. Wane ne ya ba da Isra'ila ga masu waso?Ubangiji ne kansa, shi wanda muka yi wa zunubi!Ba mu iya zama kamar yadda yake so mu yi ba,Ko mu yi biyayya da koyarwarsa da ya ba mu.

Ish 42