Ish 39:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ishaya ya ce, “Me suka gani a fāda?”Hezekiya ya amsa ya ce, “Suka ga kome da kome. Ba abin da ban nuna musu ba a ɗakunan ajiya.”

5. Sa'an nan Ishaya ya faɗa wa sarki ya ce, “Ubangiji Mai Runduna ya faɗi haka,

6. ‘Lokaci yana zuwa da za a kwashe dukan abin da yake a fādarka, da dukan abin da kakanninka suka tara har ya zuwa yau, zuwa ƙasar Babila. Ba abin da za a rage.

7. Waɗansu daga cikin zuriyarka ta kanka, za a tafi da su a maishe su babani domin su yi hidima a fādar Sarkin Babila.’ ”

8. Da sarki Hezekiya ya gane, wannan zai faru ne a bayansa, wato a zamaninsa ba kome sai lafiya, sai ya amsa ya ce, “Jawabin da ka kawo mini daga wurin Ubangiji yana da kyau.”

Ish 39