1. A wannan lokaci sai Sarkin Babila, wato Merodak Baladan, ɗan Baladan, ya ji labarin sarki Hezekiya ya yi rashin lafiya, saboda haka sai ya aika masa da wasiƙa da kuma kyautai.
2. Hezekiya kuwa ya marabci manzannin, ya kuma nunnuna musu dukiyarsa, wato azurfa da zinariya, da kayan yaji da na ƙanshi, da dukan kayayyakinsa na yaƙi. Ba abin da bai nuna musu ba a ɗakunan ajiya, da ko'ina a mulkinsa.
3. Sa'an nan annabi Ishaya ya je wurin sarki Hezekiya, ya tambaye shi ya ce, “Daga ina waɗannan mutane suka zo? Me kuma suka faɗa maka?”Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa suka zo, wato daga ƙasar Babila.”