1. Hamada za ta yi farin ciki.Furanni za su hudo a ƙasa da ba ta da amfani.
2. Hamada za ta raira waƙa da sowa don murna,Za ta zama kyakkyawa kamar Dutsen Lebanon,Da dausayi kamar filayen Karmel da Sharon.Kowa zai ga mafificiyar ɗaukakar Allah,Ya ga girmansa da ikonsa.
3. Ku ƙarfafa hannuwan da suka gaji,Da gwiwoyin da suke fama da rashin ƙarfi.