1. Ubangiji ya yi magana, ya ce, “Waɗanda suke mulkin Yahuza sun shiga uku, domin sun tayar mini. Suna aiki da shirye-shiryen da ba ni ne na yi ba, suka sa hannu a kan yarjejeniya gāba da nufina. Suna ta aikata zunubi a kan zunubi.
2. Suna tafiya Masar neman taimako, ba su shawarce ni ba. Suna so Masar ta kāre su, saboda haka suka sa dogararsu ga Sarkin Masar.
3. Amma sarkin zai rasa ikon taimakonsu, kāriyar da Masar za ta yi musu ƙarshenta masifa.
4. Ko da yake jakadunsu sun riga sun isa Zowan da Hanes, biranen Masar,
5. duk da haka jama'ar Yahuza za su yi da na sani, da suka dogara ga al'ummar da ba abar dogara ba ce, al'ummar da ba ta daɗa musu kome a lokacin da suke sa zuciya ga taimako ba.”