1. Yanzu fa Ubangiji, Ubangiji Mai Runduna, yana gab da ya kwashe kowane abin da kowane mutum da jama'ar Urushalima da na Yahuza suke dogara da su. Zai kwashe abincinsu da ruwan shansu,
2. da jarumawansu, da sojojinsu, da alƙalansu, da annabawansu, da masu yi musu duba, da manyan mutanensu,
3. da shugabannin sojojinsu, da na farar hula, da 'yan siyasarsu, da kowane mai aikin sihiri don ya sarrafa abubuwan da yake faruwa.
4. Ubangiji zai sa yaran da ba su balaga ba su mallaki jama'ar.
5. Za a yi ta cutar juna. Matasa ba za su girmama manyansu ba, talakawa ba za su girmama na gaba da su ba.
6. Lokaci yana zuwa sa'ad da mutanen wani dangi za su zaɓi ɗaya daga cikinsu, su ce, “Kai da kake da ɗan abin sawa za ka zama shugabanmu a wannan lokaci na wahala.”
7. Amma zai amsa, ya ce, “Ba ni ba dai! Ba zan iya taimakonku ba. Ba ni ma da abinci sam, ko tufafi ma. Kada ku naɗa ni shugabanku!”
8. Hakika Urushalima ta shiga uku! Yahuza tana kan fāɗuwa! Duk abin da suke faɗa, da abin da suke yi, na gāba da Ubangiji ne, a fili suke raina Allah, shi kansa.