5. Ya Urushalima, dukan baƙin da suka auka miki da yaƙi za a hure su kamar yadda iska take hure ƙura, sojojinsu kuma masu firgitarwa za a hure su kamar yadda iska take hure tattaka. Farat ɗaya ba zato ba tsammani,
6. Ubangiji Mai Runduna zai cece ki da tsawar hadiri da girgizar ƙasa. Zai aiko da hadirin iska da gagarumar wuta.
7. Sa'an nan dukan sojojin sauran al'umman da suka fāɗa wa birni inda bagaden Allah yake da yaƙi, da dukan makamansu, da kayayyakin yaƙinsu, kome da kome za su shuɗe kamar mafarki, kamar tunanin dare.
8. Dukan al'ummai da suka tattaru don su yaƙi Urushalima, za su zama kamar mutum mayunwaci da ya yi mafarki yana cin abinci, ya farka yana a mayunwacinsa, kamar wanda yake mutuwa da ƙishi ya yi mafarki yana kwankwaɗar ruwa, ya farka da busasshen maƙogwaro.
9. Ku ci gaba da aikin wautarku! Ku ci gaba da makancewarku, ku yi ta zama a makance. Ku bugu ba tare da kun sha ruwan inabi ba! Ku yi ta tangaɗi, ba don kun sha ko ɗigon ruwan inabi ba!