1. Bagaden Allah, Urushalima kanta, ƙaddara ta auko mata! Birnin da Dawuda ya kafa zango, ƙaddara ta auko mata! Bari shekara ɗaya ko biyu su zo su wuce suna shagulgulansu, suna bukukuwansu,
2. sa'an nan Allah zai kawo wa birnin wanda ake ce da shi, “Bagaden Allah,” masifa. Za a yi kuka a yi kururuwa, birnin kansa za a maishe shi bagade inda za a ƙona hadayun ƙonawa!
3. Allah zai tasar wa birnin, ya kewaye shi da yaƙi.