19. Za ta yi ta auko muku a kai a kai kowace safiya. Tilas ku sha ta dare da rana. Kowane sabon jawabin da zai zo muku daga wurin Allah, zai kawo muku sabuwar razana!
20. Za ku zama kamar mutumin da ya zama abin karin magana, wanda ya yi ƙoƙari ya kwanta a gajeren gado, ya kuma rufa da ɗan siririn bargo.
21. Ubangiji zai yi yaƙi kamar yadda ya yi a Dutsen Ferazim da a Kwarin Gibeyon domin ya aikata abin da ya yi nufin yi, ko da yake ayyukansa suna da ban al'ajabi. Zai gama aikinsa, wannan aiki kuwa mai ban al'ajabi ne.
22. Kada ku yi dariya saboda faɗakarwar da nake yi muku! Idan kuwa kun yi, zai ƙara yi muku wuya ku tsira. Na ji niyyar da Ubangiji Mai Runduna ya yi, ta ya hallaka dukan ƙasar.
23. Ku kasa kunne ga abin da nake cewa, ku mai da hankali ga abin da nake faɗa muku.
24. Manomi ba zai dinga huɗar gonakinsa har abada ba, ya yi ta shirya su domin shuka.
25. Da zarar ya shirya ƙasar yakan shusshuka ganyayen ci, kamar su kanumfari da ɗaɗɗoya, yakan kuma dasa kunyoyin alkama da na sha'ir, a gyaffan gonakin kuwa yakan shuka hatsi.
26. Ya san yadda zai yi aikinsa, gama Allah ya koya masa.