11. Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama'a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba.
12. A wannan rana Ubangiji kansa zai hukunta jama'arsa, Isra'ila, daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, tun daga Yufiretis har zuwa iyakar Masar. Zai raba tsakanin nagari da mugu.
13. A wannan rana za a busa ƙaho don a kirawo Isra'ilawan da suke zaman baƙunci a Assuriya da Masar. Za su zo su yi wa Ubangiji sujada a Urushalima a tsattsarkan dutsensa.