21. A wannan rana Ubangiji zai hukunta wa ikoki na sama, da sarakunan da suke a duniya.
22. Allah zai tattara sarakuna wuri ɗaya kamar ɗaurarru a rami, zai kulle su a kurkuku kafin lokacin da zai hukunta su ya yi.
23. Wata zai duhunta, rana ba za ta ƙara haskakawa ba, domin Ubangiji Mai Runduna yake sarauta. Zai yi mulki a Urushalima a kan Dutsen Sihiyona, shugabannin jama'a za su dubi ɗaukakarsa.