Ish 20:3-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sa'ad da aka ci Ashdod, sai Ubangiji ya ce, “Bawana Ishaya ya yi ta yawo tsira, ba kuma takalmi a ƙafarsa har shekara uku. Wannan ita ce alamar abin da zai faru a ƙasa Masar da Habasha.

4. Sarkin Assuriya zai kwashe kamammun yaƙi waɗanda ya kama a ƙasashen nan biyu, ya tafi da su tsirara. Matasa da manya kuma ba takalmi a ƙafafunsu, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar.

5. Waɗanda suke dogara ga Habasha, suna kuwa fāriya da Masar, za su ruɗe, sa zuciyarsu zai wargaje.

6. A wannan rana mutanen da suke zaune a gaɓar Filistiyawa za su ce, ‘Dubi abin da ya faru ga jama'ar da muka dogara da su don su tsare mu daga Sarkin Assuriya! Ƙaƙa za mu yi mu tsira?’ ”

Ish 20