Ish 19:22-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Ubangiji zai hukunta Masarawa, amma zai warkar da su. Za su juyo gare shi, shi kuma zai ji addu'o'insu ya warkar da su.

23. A wannan rana, za a yi wata babbar hanya tsakanin Masar da Assuriya. Mutanen ƙasashen nan biyu za su yi ta kai da kawowa tsakaninsu, al'ummai biyu za su yi sujada tare.

24. A wannan rana, za a lasafta Isra'ila tare da Masar da Assuriya, waɗannan al'ummai uku za su zama albarka ga dukan duniya.

25. Ubangiji Mai Runduna zai sa musu albarka, ya ce, “Zan sa muku albarka, ke Masar, jama'ata, da suke Assuriya wadda na halitta, da ke kuma Isra'ila zaɓaɓɓiyar jama'ata.”

Ish 19