5. Kafin a tattara 'ya'yan inabi, sa'ad da furanni duka suka karkaɗe, 'ya'yan inabi suna ta nuna, haka magabta za su hallaka Habasha a sawwaƙe kamar yadda ake faffalle rassan kurangar inabi da wuƙa.
6. Za a bar gawawwakin sojojinsu a fili domin tsuntsaye da namomin jeji su zama abincin tsuntsaye da bazara, abincin namomin jeji kuma a lokacin sanyi.”
7. A wannan lokaci Ubangiji Mai Runduna zai karɓi hadayu daga wannan ƙasa, a mafarin Kogin Nilu, wato wannan ƙaƙƙarfar al'umma mai iko, waɗannan dogayen mutane masu sulɓin jiki, waɗanda ake jin tsoronsu ko'ina a duniya. Za su zo Dutsen Sihiyona, inda ake yi wa Ubangiji Mai Runduna sujada.