Ish 17:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan shi ne jawabi a kan Dimashƙu.Ubangiji ye ce, “Dimashƙu ba za ta ƙara zama birni ba, za ta zama tsibin kufai ne kawai.

2. Za a watse a bar biranen Suriya har abada. Za su zama makiyayar tumaki da shanu. Ba wanda zai tsoratar da su.

3. Ba za a kāre Isra'ila ba, Dimashƙu kuma za ta rasa 'yancinta. Suriyawan da suka ragu za su sha wulakanci kamar mutanen Isra'ila. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗa.”

4. Ubangiji ya ce, “Rana taba zuwa, ran da girman Isra'ila zai ƙāre, fatara za ta gāje gurbin dukiyarsu.

Ish 17