1. Daga birnin Sela a hamada, mutanen Mowab za su aiko da kaiwar rago ga mai mulki a Urushalima.
2. Za su dakata a gaɓar kogin Arnon, za su yi ta kai da kawowa kamar tsuntsayen da aka kora daga sheƙunansu.
3. Suna ce wa mutanen Yahuza, “Ku faɗa mana abin da za mu yi. Ku kāre mu, ku bar mu mu huta a inuwarku mai sanyi kamar inuwar itace da tsakar rana. Mu 'yan gudun hijira ne, ku ɓoye mu inda ba wanda zai gan mu.
4. Ku bar mu mu zauna ƙasarku. Ku kāre mu daga masu neman hallaka mu.”Zalunci da hallakarwa za su ƙare, masu lalatar da ƙasar za su ƙare.
5. Sa'an nan wani daga cikin zuriyar Dawuda zai zama sarki. Zai mallaki jama'a da aminci da ƙauna. Zai aikata abin da yake daidai da hanzari, zai sa a aikata adalci.
6. Mutanen Yahuza sun ce, “Mun ji irin fāriyar da mutanen Mowab suke yi. Mun sani su masu girmankai ne, masu ruba, amma fankamarsu ta banza ce.”