1. Wannan shi ne saƙo a kan Babila, wanda Ishaya ɗan Amoz ya karɓa daga wurin Allah.
2. A kan tudun da yake faƙo ka kafa tutar yaƙi, ka ta da murya ka ba mayaƙa umarni, ka ɗaga hannu, ka ba su alamar kama yaƙi a ƙofofin birni mai alfarma.
3. Ubangiji ya kira mayaƙansa masu jin kansu, masu ƙarfin zuciya, domin su yi jahadi, su hukunta wa waɗanda suke fushi da su.
4. Ji hayaniyar da ake yi a duwatsu da amon babban taron jama'a. Amon al'ummai da mulkoki suna tattaruwa. Ubangiji Mai Runduna yana shirya mayaƙansa domin yaƙi.
5. Suna zuwa daga manisantan ƙasashe, daga kan iyakokin duniya. Ubangiji yana zuwa da fushinsa, ya lalatar da dukan ƙasar.
6. Ku yi ihu saboda shan azaba, ranar Ubangiji ta yi kusa. Ranar da Mai Iko Dukka zai kawo hallaka.
7. Hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.
8. Dukansu za su firgita, azaba za ta ci ƙarfinsu kamar mace wadda take shan azabar naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu za su cika da kunya.
9. Ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana ce ta zafin fushinsa. Za a mai da duniya jeji, a hallaka kowane mai zunubi.