1. Wannan shi ne saƙo a kan Babila, wanda Ishaya ɗan Amoz ya karɓa daga wurin Allah.
2. A kan tudun da yake faƙo ka kafa tutar yaƙi, ka ta da murya ka ba mayaƙa umarni, ka ɗaga hannu, ka ba su alamar kama yaƙi a ƙofofin birni mai alfarma.
3. Ubangiji ya kira mayaƙansa masu jin kansu, masu ƙarfin zuciya, domin su yi jahadi, su hukunta wa waɗanda suke fushi da su.
4. Ji hayaniyar da ake yi a duwatsu da amon babban taron jama'a. Amon al'ummai da mulkoki suna tattaruwa. Ubangiji Mai Runduna yana shirya mayaƙansa domin yaƙi.