Irm 9:5-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Kowane mutum yana ruɗinmaƙwabcinsa da abokinsa,Ba mai faɗar gaskiya,Sun koya wa harshensu faɗarƙarya.Suna aikata laifi,Sun rafke, sun kasa tuba.

6. Suna ƙara zalunci a kan zalunci,Yaudara a kan yaudara,Sun ƙi sanina,” in ji Ubangiji.

7. Saboda haka, Ubangiji MaiRunduna, ya faɗa cewa,“Zan tsabtace su, in gwada su,Gama me zan yi kuma sabodajama'ata?

8. Harshensu kibiya ce mai dafi, yanafaɗar ƙarya,Kowa yana maganar alheri damaƙwabcinsaAmma a zuciyarsa yana shirya masamaƙarƙashiya.

9. Ba zan hukunta su saboda waɗannanal'amura ba?Ba zan sāka wa al'umma irinwannan ba?”

Irm 9