Irm 7:32-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Domin haka, ni Ubangiji na ce, kwanaki suna zuwa lokacin da ba za a ƙara faɗar Tofet, ko kwarin ɗan Hinnom ba, amma za a kira shi Kwarin Kisa, gama za a binne mutane a Tofet domin ba sauran wuri a ko'ina.

33. Gawawwakin mutanen nan za su zama abincin tsuntsaye da na namomin jeji, ba wanda zai kore su.

34. Zan sa muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya su ƙare a biranen Yahuza da titunan Urushalima, gama ƙasar za ta zama kufai.”

Irm 7