Irm 6:27-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Ubangiji ya ce wa Irmiya,“Na maishe ka mai aunawa da maijarraba mutanenaDomin ka sani, ka aunaal'amuransu,

28. Su duka masu taurinkai ne, 'yantawaye,Suna yawo suna baza jita-jita.Su tagulla ne da baƙin ƙarfe,Dukansu lalatattu ne.

29. Ana zuga da ƙarfi,Dalma ta ƙone,Tacewar aikin banza ne,Gama ba a fitar da mugaye ba.

30. Ana ce da su ƙwan maƙerar azurfane,Gama ni na ƙi su.”

Irm 6