Irm 50:39-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

39. “Domin haka namomin jeji da diloliza su zauna a Babila,Haka kuma jiminai.Ba za a ƙara samun mazauna acikinta ba har dukan zamanai.

40. Abin da ya faru da Saduma daGwamrata,Da biranen da suke kewaye da su,Shi ne zai faru da Babila.Ba mutumin da zai zauna cikinta.

41. “Ga mutane suna zuwa daga arewa,Babbar al'umma da sarakunaSuna tahowa daga wurare masu nisana duniya.

42. Suna riƙe da baka da māshi,Mugaye ne marasa tausayi.Amonsu yana kama da rurin teku,Suna shirya don yin yaƙi da ke, yaBabila.

Irm 50