Irm 49:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Me ya sa kuke taƙama daƙarfinku,Ƙarfinku da yake ƙarewa, ku mutanemarasa aminci?Kun dogara ga dukiyarku,Kuna cewa, ‘Wane ne zai iya gāba damu?’

5. Ga shi, zan kawo muku razana dagawaɗanda suke kewaye da ku,Za a kore ku, kowane mutum zaikama gabansa,Ba wanda zai tattara 'yan gudunhijira.Ni Ubangiji Allah Mai Rundunana faɗa.

6. “Amma daga baya zan saAmmonawa su wadata kuma,Ni Ubangiji na faɗa.”

7. Ga abin da Ubangiji Mai Rundunaya faɗa a kan Edom,“Ba hikima kuma a cikin Teman?Shawara ta lalace a wurin masubasira?Hikima ta lalace ne?

Irm 49