10. Amma na tsiraita Isuwa sarai,Na buɗe wuraren ɓuyarsa,Har bai iya ɓoye kansa ba,An hallakar da mutanen IsuwaTare da 'yan'uwansa damaƙwabtansa,Ba wanda ya ragu.
11. Ka bar marayunka, ni zan rayar dasu.Matanka da mazansu sun mutu,Sai su dogara gare ni.”
12. Ubangiji ya ce, “Ga shi, waɗanda ba a shara'anta su ga shan ƙoƙon hukunci ba, za su sha shi, to, kai za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, amma lalle za ka sha shi!
13. Gama ni Ubangiji na rantse da zatina, cewa Bozara za ta zama abar tsoro, da abar dariya, da kufai, da abar la'ana. Dukan garuruwanta za su zama kufai har abada.”