1. Kafin Fir'auna ya ci Gaza da yaƙi Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan Filistiyawa.
2. Ubangiji ya ce,“Ga shi, ruwa yana tasowa dagaarewa,Zai zama kogi da yake ambaliya.Zai malala bisa ƙasa da dukan abinda yake cikinta,Da birni da mazauna cikinsa,Maza za su yi kuka,Dukan mazaunan ƙasar za su yi kuka.
3. Da jin takawar kofatan dawakai,Da amon karusai da ƙafafun karusai,Ubanni ba su juya, su dubi'ya'yansu ba,Domin hannuwansu sun yi laƙwas,