29. Da jin motsin mahayan dawakai dana maharbaKowane gari zai fashe.Waɗansu za su shiga kurama,Waɗansu kuma su hau kan duwatsu.Dukan birane za su fashe tas,Ba wanda zai zauna a cikinsu.
30. Ya ke da kike kufai marar kowa,Me kike nufi da kika ci ado da mulufi,Kike caɓa ado da kayan zinariya,Kika sa wa idanunki tozali ram?Kin yi kwalliyarki a banza,Abokan sha'anin karuwancinki sunraina ki,Ranki suke nema.
31. Na ji kuka kamar na mace wadda takenaƙuda,Na ji nishi kamar na mace a lokacinhaihuwarta ta fari,Na ji kukan 'yar Sihiyona tanakyakyari,Tana miƙa hannuwanta tana cewa,“Wayyo ni kaina, gama ina suma agaban masu kisankai!”