Irm 39:17-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Amma a ranan nan, ni Ubangiji zan cece ka, ba za a ba da kai a hannun mutanen da kake jin tsoronsu ba.

18. Gama hakika zan cece ka, ba za ka mutu ta takobi ba. Za ka sami ranka kamar ganimar yaƙi, domin ka dogara gare ni, ni Ubangiji na faɗa.’ ”

Irm 39