19. Ina annabawanku waɗanda suka yi maka annabci cewa, ‘Sarkin Babila ba zai kawo wa ƙasarku yaƙi ba?’
20. Yanzu ya maigirma sarki, ina roƙonka ka ji wannan roƙo da nake yi maka, kada ka mai da ni a gidan Jonatan magatakarda, domin kada in mutu a can.”
21. Sai sarki Zadakiya ya ba da umarni, suka sa Irmiya a gidan waƙafi. Aka riƙa ba shi malmalar abinci daga unguwar masu tuya kowace rana, har lokacin da abinci ya ƙare duka a birnin. Haka kuwa Irmiya ya zauna a gidan waƙafi.