14. Sai dukan sarakunan suka aiki Yehudi ɗan Netaniya, ɗan Shelemiya, ɗan Kushi, ya faɗa wa Baruk ya kawo littafin nan da ya karanta wa jama'a. Sai Baruk ɗan Neriya ya ɗauki littafin ya je wurinsu.
15. Suka ce masa ya zauna, ya karanta musu littafin. Baruk kuwa ya karanta musu.
16. Da suka ji dukan maganar, suka dubi juna a firgice, suka ce wa Baruk, “Ai, sai mu faɗa wa sarki wannan magana.”
17. Suka kuma tambayi Baruk, suka ce, “Ka faɗa mana yadda ka yi ka rubuta wannan magana. Ya yi maka shibta ne?”
18. Sai Baruk ya ce musu, “Ya yi mini shibtar dukan wannan magana ne, na kuwa rubuta su da tawada a takarda.”
19. Sarakunan kuwa suka ce wa Baruk, “Ka tafi, da kai da Irmiya ku ɓuya kada ku bari kowa ya san wurin da kuke.”
20. Suka tafi zauren sarki bayan sun ajiye littafin a ɗakin Elishama, magatakarda, suka sanar da sarki dukan abin da yake cikin littafin.
21. Sarki ya aiki Yehudi ya je ya kawo littafin. Sai ya je ya ɗauko littafin daga ɗakin Elishama magatakarda. Yehudi kuwa ya karanta wa sarki tare da dukan sarakunan da suke tsaye kewaye da sarkin.
22. A watan tara ne, sarki kuwa yana zaune a gidansa na rani, ga wuta tana ci cikin kasko a gabansa.
23. Da Yehudi ya karanta sakin layi uku ko huɗu sai sarki ya sa wuƙa ya yanke su, ya zuba a wutar da take ci a kasko, da haka ya ƙone littafin duka.
24. Duk da haka da sarkin da barorinsa suka ji maganar, ba wanda ya ji tsoro, balle su keta rigunansu don baƙin ciki.
25. Ko da yake Elnatan, da Delaiya, da Gemariya, sun faɗa wa sarki kada ya ƙone littafin, amma ya yi biris da su.
26. Sarki ya umarci Yerameyel ɗan sarki, da Seraiya ɗan Azriyel da Shelemiya ɗan Abdeyel, su kamo Baruk magatakarda da annabi Irmiya, amma Ubangiji ya ɓoye su!
27. Bayan da sarki ya ƙone littafin da Baruk ya rubuta ta wurin shibtar da Irmiya ya yi masa, sai Ubangiji ya yi wa Irmiya magana, ya ce,
28. ya ɗauki wata takarda ya rubuta dukan maganar da take cikin littafin da Yehoyakim Sarkin Yahuza, ya ƙone.
29. Zai kuma ce wa Yehoyakim Sarkin Yahuza, “Haka Ubangiji ya ce maka, ka ƙone littafin, kana cewa, ‘Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle Sarkin Babila zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?’