Irm 29:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Gama na san irin shirin da na yi muku, ni Ubangiji na faɗa. Shirin alheri, ba na mugunta ba. Zan ba ku gabata da sa zuciya.

12. Sa'an nan za ku yi kira a gare ni, ku yi addu'a a wurina, zan kuwa ji ku.

13. Za ku neme ni ku same ni, idan kun neme ni da zuciya ɗaya.

14. Za ku same ni, ni Ubangiji na faɗa, zan mayar muku da arzikinku, in tattaro ku daga cikin dukan al'ummai da dukan wurare inda na kora ku, ni Ubangiji na faɗa, zan komo da ku a wurin da na sa a kwashe ku a kai ku zaman talala.’

15. “Domin kun ce, Ubangiji ya ba ku annabawa a Babila,

16. ku ji abin da Ubangiji ya faɗa a kan sarkin da ya hau gadon sarautar Dawuda, da a kan dukan jama'ar da suke zaune a wannan birni, wato a kan danginku waɗanda ba a kwashe su zuwa zaman talala ba.

17. Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Ga shi, zan aiko musu da takobi, da yunwa, da masifa, zan maishe su kamar ruɓaɓɓen ɓaure waɗanda suka lalace ƙwarai, har ba su ciwuwa.

18. Zan fafare su da takobi, da yunwa, da masifa. Zan maishe su abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya. Za su zama abin la'ana, da abin razana, da abin raini, da abin zargi, ga dukan al'ummai, inda na kora su.

Irm 29