Irm 25:32-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Ga masifa tana tahowa dagaal'umma zuwa al'umma,Hadiri kuma yana tasowa dagadukan manisantan wurare naduniya.

33. Waɗanda Ubangiji ya kashe awannan rana,Za su zama daga wannan bangonduniya zuwa wancan.Ba za a yi makoki dominsu ba,Ba kuwa za a tattara gawawwakinsua binne ba.Za su zama taki ga ƙasa.

34. “Ku yi makoki, ku yi kuka, kumakiyaya,Ku yi ta birgima a cikin toka kuiyayengijin garke,Gama ranar da za a yanka ku daranar da za a warwatsa ku ta zo,Za ku fāɗi kamar zaɓaɓɓen kasko.

35. Ba mafakar da ta ragu dominmakiyaya,Iyayengijin garken ba za su tsira ba.

Irm 25