Irm 25:14-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Al'ummai da yawa da manyan sarakuna za su bautar da su, ni kuwa zan yi musu sakayya bisa ga ayyukan hannuwansu.’ ”

15. Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce mini, “Ka karɓi ƙoƙon ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al'umman da na aike ka gare su, su sha.

16. Za su sha, su yi tangaɗi su yi hauka saboda takobin da zan aiko a cikinsu.”

17. Sai na karɓi ƙoƙon daga wurin Ubangiji, na sa dukan al'umman da Ubangiji ya aike ni gare su, su sha daga cikinsa.

18. Urushalima, da biranen Yahuza, da sarakunanta, da shugabanninta, za su zama kango da abin ƙyama da abin raini, da abin la'ana. Haka yake a yau.

19-26. Ga lissafin sauran da za su shaƙoƙon.Fir'auna Sarkin Masar da kumabarorinsa, da sarakunansa,Dukan jama'arsa, da dukanbaƙin da suke tare da su,dukan sarakunan ƙasar Uz,dukan sarakunan ƙasarFilistiyawa, wato Ashkelon, daGaza, da Ekron, da saura naAshdod,Edom da Mowab, da 'ya'yanAmmon maza,dukan sarakunan Taya, da dukansarakunan Sidon,dukan sarakunan da suke gaɓarBahar Rum da waɗanda suke atsibiran tekun,Dedan, da Tema, da Buz, dadukan waɗanda suke yi wakansu sanƙo,dukan sarakunan Arabiya,dukan sarakunan tattarmukanmutane da suke zaune ahamada,dukan sarakunan Zimri, da dukansarakunan Elam, da dukansarakunan Mediya,dukan sarakunan arewa, na nesada na kusa bi da bi.Dukan mulkokin da suke fuskar duniya za su sha daga ciki. Daga nan sai Sarkin Babila a bayansu duka, zai sha nasa.

27. “Za ka kuma faɗa musu cewa, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ku sha, ku bugu, ku yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku tashi saboda takobin da zan aiko muku.’

Irm 25