8. Firistoci kuma ba su ce, ‘Ina UbangijiYake?’ ba.Masanan shari'a ba su san ni ba.Masu mulki sun yi mini laifi,Annabawa sun yi annabci da sunanBa'al,Sun bi waɗansu abubuwa marasaamfani.”
9. “Domin haka, ni Ubangiji zangabatar da ku gaban shari'a,Ku da 'ya'yanku, da 'ya'yan'ya'yanku, wato jikokinku.
10. Ku haye zuwa tsibirin Kittim wajenyamma, ku gani,Ku aika zuwa Kedar wajen gabas, kuduba da kyau,A dā an taɓa yin wani abu haka?