22. Bari a ji kururuwa daga gidajensu,Saboda maharan da ka aika musufarat ɗaya,Gama sun haƙa rami don in fāɗa,Sun kafa wa ƙafafuna tarkuna.
23. Amma ya Ubangiji,Ka san dukan maƙarƙashiyarsu,su kashe ni,Kada ka gafarta musu muguntarsu,kada kuma ka shafe zunubinsudaga gabanka.Ka sa a jefar da su daga gabanka,Ka yi da su sa'ad da kake fushi!”