21. Me za ku ce sa'ad da aka naɗa mukushugabanni,Waɗanda ku da kanku kuka koyamusu, suka zama abokanku?Ashe, azabai ba za su auko muku baKamar yadda sukan auko wa macemai naƙuda?
22. Idan kun ce a zuciyarku,‘Me ya sa waɗannan abubuwa sukasame mu?’Saboda yawan zunubanku ne,Shi ya sa an tone tsiraicinku,Aka wahalshe ku.
23. Mutumin Habasha zai iya sākelaunin fatar jikinsa?Ko kuwa damisa za ta iya sākedabbare-dabbarenta?Idan haka ne, ku kuma za ku iya yinnagarta,Ku da kuka saba da yin mugunta.
24. Zan warwatsar da kuKamar yadda iskar hamada takewatsar da ƙaiƙayi.”