Irm 10:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya jama'ar Isra'ila, ku ji jawabin da Ubangiji yake yi muku.

2. Ubangiji ya ce,“Kada ku koyi abubuwan daal'ummai suke yi,Kada ku ji tsoron alamun da suke asama,Ko da yake al'ummai suna jintsoronsu.

3. Gama al'adun mutane na ƙarya ne,Daga cikin jeji aka sare wani itace,Gwanin sassaƙa ya sassaƙa shi dagizago.

4. Mutane sukan yi masa ado na azurfada zinariya,Sukan ɗauki guduma su kafa shi daƙusoshi,Don kada ya motsa.

5. Gumakansu dodon gona suke, acikin gonar kabewa,Ba su iya yin magana,Ɗaukarsu ake yi domin ba su iyatafiya!Kada ku ji tsoronsu.Gama ba su da ikon aikata muguntako alheri.”

6. Ya Ubangiji, ba wani kamarka,Kai mai girma ne,Sunanka kuma yana da girma daiko.

7. Wane ne ba zai ji tsoronka ba, yaSarkin dukan al'ummai?Ka isa a ji tsoronka,Gama babu kamarka a cikin dukanmasu hikima na al'ummai,Da kuma cikin dukan mulkokinsu,Ba wani kamarka.

8. Dukansu dakikai ne wawaye,Koyarwar gumaka ba wani abu bane, itace ne kawai!

9. An kawo fallayen azurfa dagaTarshish,Da zinariya kuma daga Ufaz,Aikin gwanaye da maƙeranzinariya.Tufafinsu na mulufi ne da shunayya,duka aikin gwanaye.

Irm 10