Hab 2:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Zan tsaya a wurin tsayawata,In zauna kuma a kan hasumiya,In jira in ji abin da zai ce mini,Da abin da zai amsa a kan kukata.

2. Sai Ubangiji ya ce mini,“Ka rubuta wahayin da kyau a kan alluna,Yadda kowa zai karanta shi a sawwaƙe.

3. Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa,Yana gaggautawa zuwa cikarsa,Ba zai zama ƙarya ba.Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri,Hakika zai zo, ba zai makara ba.

4. Wanda zuciyarsa ba daidai take ba, zai fāɗi,Amma adali zai rayu bisa ga bangaskiyarsa.

Hab 2