Gal 4:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ana nufin, magaji, muddin yana yaro bai fi bawa ba, ko da yake yana da mallakar dukkan kome.

2. A hannun iyayen goyo da wakilai yake har zuwa ranar da mahaifinsa ya sa.

3. Haka yake a gare mu, wato sa'ad da muke kamar yara, a cikin ƙangin bautar al'adun duniya muke.

Gal 4