24. Da zinariya tsantsa na talanti ɗaya ya yi alkukin da kayayyakinsa duka.
25. Ya yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, shi murabba'i ne, tsayinsa kuma kamu biyu ne, zankayensa kuwa a haɗe suke da shi.
26. Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, da bisansa, da kewayen gyaffansa, da zankayensa. Ya kewaye shi kuma da dajiya ta zinariya.
27. Ya sa masa ƙawane biyu na zinariya a gyaffansa a ƙarkashin dajiya daura da juna don a zura sandunan ɗaukarsa.
28. Ya kuma yi sanduna biyu da itacen ƙirya, sa'an nan ya dalaye su da zinariya.
29. Ya yi tsattsarkan mai na keɓewa da kuma turare mai ƙanshi yadda mai yin turare yakan yi.