Fit 28:8-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Za a yi mata abin ɗamara da irin kayan da aka yi falmaran, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Za a yi mata saƙar gwaninta.

9. A kuma ɗauki duwatsu biyu masu daraja, a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a kai.

10. Sunaye shida a kowane dutse bi da bi bisa ga haihuwarsu.

Fit 28