Fit 28:3-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ka kuma yi magana da gwanayen sana'a duka waɗanda na ba su fasaha, don su ɗinka wa Haruna tufafi, gama za a keɓe shi ya zama firist ɗina.

4. Waɗannan su ne irin tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da falmaran, da taguwa, da zilaika, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan'uwanka, Haruna, da 'ya'yansa tufafi tsarkaka, don su zama firistoci masu yi mini aiki.

5. Sai su yi amfani da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.

6. “Za su yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya da mulufi, da lallausan zaren lilin, aikin gwani.

7. Za a yi mata kafaɗa biyu, sa'an nan a haɗa su a karbunsu.

8. Za a yi mata abin ɗamara da irin kayan da aka yi falmaran, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Za a yi mata saƙar gwaninta.

9. A kuma ɗauki duwatsu biyu masu daraja, a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a kai.

10. Sunaye shida a kowane dutse bi da bi bisa ga haihuwarsu.

11. Za a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a bisa duwatsun nan kamar yadda mai yin aiki da lu'ulu'u yakan zana hatimai. Za a sa kowane dutse a cikin tsaiko na zinariya.

Fit 28