Fit 28:16-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ƙyallen maƙalawa a ƙirji zai zama murabba'i, a ninke shi biyu tsawonsa da fāɗinsa su zama kamu ɗaya ɗaya.

17. Sai a yi jeri huɗu na duwatsun a kanta. A jeri na fari, a sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu.

18. A jeri na biyu, a sa turkos, da saffir, da daimon.

19. A jeri na uku, a sa yakinta, da idon mage, da ametis.

Fit 28