29. Amma idan san ya saba fafarar mutane, aka kuma yi wa mai shi kashedi, amma bai kula ba, har san ya kashe ko mace ko namiji, sai a jajjefi san duk da mai shi.
30. Idan an yanka masa diyya, sai ya biya iyakar abin da aka yanka masa don ya fanshi ransa.
31. Haka kuma za a yi idan san ya kashe ɗan wani ko 'yar wani.