26. Ya ce, “In za ku himmantu ku yi biyayya da ni, ni da nake Ubangiji Allahnku, sai ku aikata abin da yake daidai a gare ni, ku kuma kiyaye umarnaina da dokokina duka, to, ba zan sa muku cuce-cuce irin waɗanda na sa wa Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”
27. Daga nan suka je Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa goma sha biyu, da itatuwan giginya saba'in. A nan suka yi zango a bakin ruwa.