Filib 4:17-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Ba cewa, don ina neman kyautarku ba ne, a'a, nemar muku amfani nake yi, a ƙara a kan ribarku.

18. An biya ni sarai, har fi. Bukatata ta biya, da na karɓi kyautar da kuka aiko mini ta hannun Abafaroditas, baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.

19. Allahna kuma zai biya muku kowace bukatarku daga cikin yalwar ɗaukakarsa da take ga Almasihu Yesu.

20. Ɗaukaka tā tabbata ga Allahnmu, Ubanmu, har abada abadin. Amin! Amin!

21. Ku gai da kowane tsattsarka cikin Almasihu Yesu. 'Yan'uwan da suke tare da ni suna gai da ku.

22. Dukan tsarkaka suna gai da ku, tun ba ma na fadar Kaisar ba.

23. Alherin Ubangiji Yesu Almasihu yă tabbata a zukatanku.

Filib 4