Far 8:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Allah kuwa ya tuna da Nuhu da dukan dabbobin gida da na jeji waɗanda suke cikin jirgi tare da shi. Allah ya sa iska ta hura bisa duniya, ruwaye suka janye.

2. Maɓuɓɓugan zurfafa da tagogin sammai suka rufe, aka dakatar da ruwa daga sammai,

3. ruwa ya yi ta janyewa daga duniya. Bayan kwana ɗari da hamsin sai ruwa ya ragu.

4. Ya zama kuwa a ran sha bakwai ga wata na bakwai, sai jirgin ya tafi ya tsaya bisa kan dutsen Ararat.

5. Ruwa ya yi ta raguwa har wata na goma. A ran ɗaya ga wata na goma, sai kawunan duwatsu suka ɓullo.

6. A ƙarshen kwana arba'in Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi,

7. sai ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har lokacin da ruwan ya ƙafe a duniya.

8. Sai kuma ya aiki kurciya ta gani ko ruwa ya janye,

9. amma kurciyar ba ta sami inda za ta sauka ba, sai ta komo wurinsa cikin jirgi, gama har yanzu ruwa na rufe ƙasa duka. Sai ya miƙa hannunsa ya ɗauko ta ya shigar da ita cikin jirgi tare da shi.

10. Ya jira kuma har kwana bakwai, sai kuma ya sāke aiken kurciyar daga cikin jirgin.

11. Kurciyar kuwa ta komo wurinsa da maraice, ga shi kuwa, a bakinta sabon tohon zaitun wanda ta tsinko, domin haka Nuhu ya gane ruwa ya janye daga duniya.

12. Sai ya sāke dakatawa har kwana bakwai, ya kuma aiki kurciya, amma ba ta ƙara komowa wurinsa ba.

Far 8