Far 49:16-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. “Dan zai zama mai mulki gamutanensaKamar ɗaya daga cikin kabilanIsra'ila.

17. Dan zai zama maciji a gefen hanya,Zai zama kububuwa a gefen turba,Mai saran diddigen dokiDon mahayin ya fāɗi da baya.

18. Ina zuba ido ga cetonka, yaUbangiji.

19. “Gad, 'yan fashi za su kai masa hari,Shi kuwa zai runtume su.

Far 49