Far 49:10-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Yana riƙe da sandan mulkinsa,Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa,Har Shilo ya zo.Zai mallaki dukan jama'o'i.

11. Zai ɗaure aholakinsa a kurangarinabi,A kuranga mafi kyau,Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi,Ruwan inabi ja wur kamar jini.

12. Idanunsa za su yi ja wur saboda shanruwan inabi,Haƙoransa kuma su yi fari fatsaboda shan madara.

13. “Zabaluna zai zauna a gefen teku,Zai zama tashar jiragen ruwa,Kan iyakarsa kuma zai kai harSidon.

14. “Issaka alfadari ne ƙaƙƙarfa,Ya kwanta a miƙe tsakaninjakunkunan shimfiɗa.

Far 49